Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero zai Ziyarci kasashen Gambia da Senegal domin gudanar da ziyarar aiki ta mako guda Sakamakon gayyatar da majalisar dattawan kasar Gambia ta yi masa.
Wata sanarwa daga Masarautar kano ta ce, matakin farko na ziyarar da za ta kai shi Gambiya za ta ba shi damar halartar bikin zagayowar ranar samun ‘yancin kan kasar, wanda za a gudanar a ranar Juma’a, kuma sarkin na Kano zai kasance a matsayin babban bako na musamman.
An kuma shirya Sarkin zai halarci Sallar Juma’a tare da Shugaban kasar Gambia, Adama Barrow daga bisani kuma ya kai masa ziyarar ban girma.
Ziyarar a Gambia za ta kare ne da gagarumin liyafar karrama daga majalisar dattawan kasar ta Gambia, wadda za ta shiryawa Sarkin na kano.
Sarkin Kanon, Alhaji Aminu Ado Bayero, zai je ne tare da rakiyar Ambasada Ahmed Umar, Dan Malikin Kano, Isa Sanusi, shugaban cibiyar Kasuwanci ta Kano, Alhaji Dalhatu Abubakar da wasu jami’an cibiyar guda biyu, za su wuce Dakar babban birnin kasar Senegal.
Ana kuma sa ran sarkin zai kai ziyarar ban girma ga shugaban kasar Senegal Macky Sall.