Cibiyar Yaki da Cututtuka ta Najeriya NCDC, ta ce barkewar zazzabin Lassa ya yi sanadin mutuwar mutane 59 tun daga farkon shekarar nan.
A wani rahoto da ta fitar a ranar Laraba, cibiyar ta ce an samu mutane 358 da aka tabbatar sun kamu da cutar a bana a jihohi 19, da kananan hukumomi 65 na kasar nan.
Rahoton ya ce sabbin ma’aikatan kiwon lafiya bakwai sun kamu da cutar a jihohin Bauchi, Ondo da Edo.
An kuma bayyana cewa a cikin mako na shida, adadin wadanda aka tabbatar sun karu daga 58 a mako na biyar, na shekarar 2022 zuwa 77.
“An ruwaito wadannan suka kamu sun fito ne daga Ondo, Edo, Bauchi, Ebonyi, Taraba, Enugu, Benue, Kogi, Nasarawa, Jihohin Neja, da babban birnin tarayya (FCT).
“A dunƙule daga mako ɗaya zuwa mako na shida, na 2022; An ba da rahoton mutuwar mutane 59 tare da adadin masu mutuwa (CFR) na kashi 16.5 cikin ɗari wanda ya yi ƙasa da wadanda suka mutu a daidai wannan lokacin a cikin shekarar 2021 (kashi 22.9)”.
NCDC ta ce an bude cibiyar kula da Marasa Lafiya cikin gaggawa ta kasa da kasa da ke da alaka da zazzabin Lassa da dama domin daidaita ayyukan magace cutar a dukkan matakai.