By Abbas Yakubu Yaura
Wasu ‘yan daba da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne da yammacin ranar Juma’a sun tarwatsa wata motar bas kirar Toyota Hiace mallakar hukumar kula da tsaftar yankunan karkara da ruwan sha ta gwamnatin jihar Osun.
An bayyana cewa maharan sun bi sahun motar bas din da aka ce ta nufi Osogbo mai nisa da hedikwatar ‘yan sanda ta Zone XI.
Bidiyon lamarin da wakilinmu ya samu ya nuna cewa maharan sun farfasa gilashin bayan motar, da kuma gilashin gefen ta.
Sai dai kuma ba a bayyana sunayen mutanen da ke cikin motar ba a cikin bidiyon na tsawon dakika 39.
Bas din mai lamba 52C-09 OS, kuma tana dauke da rubutu www.ruwesa.osun.gov.ng.
Ana iya jin wata murya a cikin bidiyon tana cewa maharin “ya raunata direban bas din.”
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto babu wani jami’in gwamnatin jihar Osun da ya bayar da amsa kan lamarin.
Harin dai ya faru ne sa’o’i kadan kafin gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar APC na jihar a ranar Asabar.