Alamu sun nuna cewa akwai yiwuwar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta dage shirin gudanar da zaben 2023, a lokacin da ta tsara gudanarwa, idan har shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi aiki da dokar zaben da aka aike masa bayan ranar 22 ga watan Fabrairun 2022.
Bayan babban zaben 2019, INEC, wadda ita ce alkalan zabe da doka ta ba su ikon tsayar da ranakun zabe, ta tsayar da ranar 18 ga Fabrairu, 2023 da za a gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya na 2023.
Sai dai kusan shekara guda da gudanar da zaben shugaban kasa, har yanzu INEC ba ta fitar da ka’idojin yadda za a gudanar da zaben ba, saboda tana jiran wani sabon tsarin zabe.
Kamar yadda sashe na 28 (1) na kundin dokar zabe na 2022 ya nuna, ana bukatar INEC ta fitar da sanarwar zaben kasa da kwanaki 360 kafin ranar da aka sanya domin yin zabe.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta tsayar da ranar 18 ga watan Fabrairun 2023 domin gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya na 2023.