Mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, DCP, Abba Kyari da ake tsare da shi ya maka gwamnatin tarayya a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja yana kalubalantar ci gaba da tsare shi da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ke yi.
A karar mai lamba FHC/ABJ/CS/182/22, Kyari wanda a halin yanzu aka dakatar da shi daga kasancewa jami’in rundunar ‘yan sandan Najeriya na neman kotu data bada umarnin gaggauta sakin shi.
“A madadin, DCP da aka dakatar, wanda hukumar NDLEA ke tsare da shi bisa zarginsa da hannu a safarar miyagun kwayoyi yana son kotu ta bada belinsa a cikin yanayi na sassauci.” Kamar yadda Takaddar karar ta nuna.
A nasaran cewa Mai Shari’a Iyang Eden Ekwo ne zai shigar da karar da Kyari ya shirya a kowani lokaci a yau Litinin
A kwai Karin bayani….