Sanata mai wakiltar Kano ta Arewa, Barau I. Jibrin ya karyata labarin da wani sashi na kafafen yada labarai ke yadawa kan ganawarsa da Abdulaziz Ganduje, dan Gwamna Abdullahi Ganduje a karshen mako.
A karshen makon da ya gabata ne kafafen sada zumunta da wasu kafafen yada labarai na yanar gizo suka yi ta yada labarin ganawar Sanatan da Abdulaziz Ganduje suna masu rade-radin cewa taron sunyi shine domin hakurkurtar da Sanata game da kudurinsa na son tsayawa takarar gwamna.
Labarin ya nuna cewa Gwamna Abdullahi Ganduje ya aika dansa ya gana da Barau Jibrin don ya tsaya takarar Sanata a 2023 maimakon kujerar Gwamna.
Sanata Barau Jibrin mamba ne na kungiyar G7 ta jam’iyyar APC a Kano.
Bangaren dai ya yi ta fafatawa da tsagin Gwamna Abdullahi Ganduje kan harkokin jam’iyyar da ya kai ga caca baki da batutuwan da suka shafi kotu.