Daruruwan mutane ne suka koma gidajensu bayan da wata gobara ta barke a wani sansanin ‘yan gudun hijira da ke karamar hukumar Mafa a jihar Borno a ranar Laraba, kamar yadda majiya ta bayyana.
Wannan dai na zuwa ne makonni kadan da suka gabata bayan da gobara ta kone Wani sansanin ‘yan gudun hijira na Muna Al-Barnawi da ke Maiduguri.
Lamarin dai ya faru makonni biyu da suka gabata ya yin da gobarar ta yi sanadiyar lalata gidaje sama da 3,000.
An ruwaito cewa gobarar ta tashi ne bayan karfe 12 na rana kuma ta lalata gidaje na wucin gadi da ba a tantance adadinsu ba.
Wata majiyar jin kai ta shaida wa wakilin Jaridar Daily Truat cewa, gobarar ta kone kayan abinci da sauran kayayyaki masu daraja.
“Har yanzu ba mu san musabbabin tashin gobarar ba amma sama da daruruwan matsugunan wucin gadi ne suka lalace. Muna aiki a kai yanzu.”
Kazalika rahotanni na nuna cewa bayan kimanin awa daya ne jami’an hukumar kashe gobara na jihar Borno suka Isa wurin domin kashe gobarar