By Abbas Yakubu Yaura
Sojoji 15, dan sanda daya da fararen hula da ba a tantance adadinsu ba, an ce sun rasa rayukansu a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai wa ayarin motocin mataimakin gwamnan jihar Kebbi, Kanar Samaila Yonbe (mai ritaya) hari.
Da yake magana da jaridar PUNCH, wani dan asalin yankin, Musa Mohammed, ya ce maharan sun kuma kwashe kakin sojan da aka kashe da kuma bindigun su.
Mohammed ya kara da cewa an ajiye gawarwakin sojojin da aka kashe a babban asibitin Sir Yahaya da ke Birnin Kebbi.
A cewarsa, mataimakin gwamnan yana kan hanyarsa ta zuwa kauyen Kenya ne tare da kwamandan barikin soji na Zuru domin jajanta wa mutanen kauyen bisa kashe ‘yan banga 67 da ‘yan fashin daji suka yi a ranar Litinin da ta gabata.
Mohammed ya kara da cewa wasu ‘yan fashin dajin sun kai wa mataimakin gwamnan hari ne a kauyen Kenya da misalin karfe 8 na daren ranar Talata bayan da suka samu labarin cewa shi (mataimakin gwamnan) yana kauyen.
“Nan da nan ‘yan fashin suka isa kauyen, suka bude wa ayarin mataimakin gwamnan wuta sannan jami’an tsaron da ke tare da shi su ma suka mayar da martani,” inji shi.
Ya kara da cewa ‘yan fashin dajin wadanda suke da yawa sun yi galaba a kan ayarin mataimakin gwamnan, inda suka kashe jami’an soji 15 da dan sanda guda.
Sannan ya ce fararen hula da ba a tantance adadinsu ba suma sun rasa rayukansu yayin harin.
Kazalika ya bayyana cewa mataimakin gwamnan ya tsallake rijiya da baya amma babban jami’in tsaron sa, SP Nafiu Abubakar yana cikin wadanda aka kashe nan take.
Ba a samu damar jin ta bakin babban sakataren yada labaran mataimakin gwamnan, Abdullahi Yalmo domin jin ta bakinsa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.