Hukumar yaki da saffarar bi-adama ta kasa (NAPTIP), ta ceto mutane 35 daga hannun wasu da Ake zargin masu safarar mutane zuwa Jamhuriyar Nijar.
Ko’odinetan hukumar na shiyyar Abdullahi Babale ne ya bayyana haka a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN a Kano.
Ya ce an mika wadanda aka ceto ga Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NAPTIP) da ke Kongolam International Border Post, Mai Adua a Jihar Katsina.
“Wadanda aka akayi yunkurin saffarar su, sun hada da maza shida da mata 29, masu shekaru tsakanin biyar zuwa 42”
Ya kara da cewa an yi jigilar wadanda abin ya shafa ne da aka dauko su daga jihohin Ondo, Legas, Enugu, Anambra, Oyo, Imo, Ogun, Ekiti, Edo, Osun, Kogi da kuma Abia.
“Wadanda abin ya shafa suna kan hanyarsu ta zuwa Turai ta kan iyakar Najeriya,” ya kara da cewa hukumar ta fara bincike kan lamarin.