Tsohon Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar ya bayyana dalilan da suka sanya yaƙi ɗaukar Bola Tinubu a matsayin abokin Takarar shi a Shekarar 2007, a lokacin da suke cikin Jam’iyyar AC.
Atiku ya bayyana cewar yaƙi ɗaukar Tinubu abokin takarar shi, a dalilan wasu sharuɗɗa daya gindaya mashi, kafin ya yarda.
Yayi wannan jawabin a lokacin taron shi da Kwamitin gudanarwa na Jam’iyyar PDP a Abuja a jiya (Litinin).
KARANTA WANNAN LABARIN: Wata Sabuwa: Wutar Lantarki ta Inganta a ƙarƙashin Mulkin Buhari – Inji Hadimin Buhari Bashir Ahmed
Ɗan Takarar Jam’iyyar PDP ya bayyana cewar ya ɗauki Ben Obi abokin takarar shi, sakamakon wasu sharuɗɗa da Tinubu ya gindaya mashi.
A cewar Atiku “a lokacin da na shiga Jami’yar AC, wadda Abokina Bola ta shiga, ya gindaya man wasu sharuɗɗa kafin ya bani tikitin tsayawa takara, domin in maida shi Abokin takarar sa.
“Nace a’a, bazan sanya ka zamanto Mataimaki na ba, a dalilin haka na ɗauki Sanata Ben.”
Wazirin Adamawa ya kuma ƙara dacewa, PDP ba zata iya zama tana ƙara adawa a wasu Shekaru 8 masu zuwa.
Atiku ya jaddada cewa, saka zama ba tare da Jam’iyyar ta samu nasara ba, na Shekaru 8 zai haifar da mutuwar Jam’iyyar,” Inji shi.