A ranar Alhamis din Nan wata tankar mai dauke da ma n fetur ta fashe a mahadar Ijora Pallete daura da rukunin gidaje na jihar Legas da ke Ijora Badiya a jihar Legas.
Fashewar ta faru ne da karfe 1.30 na rana.
Wani ganau ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na NAN cewa tankar ta na yoyo ne, wasu da ke wucewa ne suka jawo hankalin direban kan lamarin.
Shaidan gani da idon ya ce sakamakon haka direban ya sauka ya yi yunkurin yin amfani da na’urar kashe gobara a kan tankar kafin ta fashe.
Jami’an kwana-kwana da tawagar ‘yan sandan Ijora Badiya sun yi kasa a wurin da lamarin ya faru don kare rayuka da dukiyoyi.
Daga karshe dai sun kashe gobarar kuma ba a samu asarar rai ba a hadarin.
Yan sanda sun karkatar da ababen hawa daga hanyar domin hana cunkoson ababen hawa da kuma hana ’yan mata gari, su far wa mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.
A cewar wani jami’in ‘yan sandan da ya nemi a sakaya sunansa, ‘yan sandan sun yi gaggawar kai daukin a wurin inda suka tuntubi hukumar kashe gobara wacce ita ma ta dauki matakin gaggawa.
Comments 1