Akalla mutane 46 ne aka yi garkuwa da su a Agunu Dutse dake unguwar Agunu a karamar hukumar Kachia ta jihar Kaduna.
Da yake zantawa da Jaridar Daily Trust, wani mazaunin garin Mai suna Maurice Clement Tanko (dake Galadiman Agunu Dutse), ya ce masu garkuwa da mutane sun kai farmaki yankin ne da misalin karfe 12:30 na sanyin safiyar ranar Alhamis.
“Da misalin karfe 12:30 na safe ne jami’an sa kai na mu suka lura da wani motsi da ba a saba gani ba a wajen yankin, dake da nisan mil 200 da kuma Wani tartsatsin wutar lantarki a matsayin hanyar sadarwa amma sakamakon ,” in ji shi.
“Kuma masu garkuwa da mutanen sun yi ta gudanar da aiyukan su na tsawon mintuna 10-20 amma sun lura cewa ‘yan banga na cikin shirin ko-ta-kwana.”
Ya kara da cewa wani mutum daya daga cikin al’ummar yankin mai suna Abubakar Sule ya samu rauni yayin harin, amma a yanzu haka yana samun kulawa a wani asibiti.
Jami’in hulda da jama’a na ’yan sandan, ASP Muhammed Jalige, bai amsa tambayoyin da wakilin Jaridar Daily trust yai masa ba kan harin ba.