Kaduna: Ƴan bindiga sun kashe mutane 23, sun sace wasu da yawa a Giwa
Ƴan bindiga a daren Talata da daddare sun kashe mutane 23 tare da sace wasu da raunata wasu da harbin bindiga a hare-hare a ƙauyuka guda biyu a Ƙaramar Hukumar Giwa ta Jahar Kaduna.
Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta ta bada tahoton cewa ƴan bindiga sun kai hari a ƙauyuka guda 9 a Ƙaramar Hukumar Giwa, tare da kashe mutane 50, a yayinda suka sace wasu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ina jin Tausayin Najeriya, duk da mai hura ƙwallon baya goyon bayan mu — Cewar Kocin Ghana, Otto Addo
Harin ranar Talata da daddare shine na huɗu da Suka kai a Ƙaramar Hukumar Giwa, tun watan Maris na Shekarar 2022.
Wani Mazaunin Al’ummomin ya shaida cewar a ranar Laraba, ƴan bindiga sun zo da yawa tare da harbi a saman iska.
A dalilin haka, mutane da dama da suka gudu domin tsira da lafiyar su, harbin bindigar ya iske su.
Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar Kaduna ASP Mohammed Jalige ba’a same shi ba domin magana.