Fasinjoji bakwai da suka hada da ‘yan mata biyu ne suka mutu a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da su a hanyar Ogbomosho zuwa Ilorin a jihar Kwara.
Hatsarin wanda ya afku da misalin karfe 3:00 na safiyar ranar Lahadi ya bar wasu mutane 21 da munanan raunuka.
An ruwaito cewa babbar motar bas din kirar Mazda mai daukar mutane 18 mai lamba ZUR 159 XJ tana kan hanyar zuwa Legas ne a lokacin da tayar motar ta fashe a kauyen Ote da ke karamar hukumar Asa ta jihar sakamakon daukar kaya fiye da kima da ya yi sanadiyyar hatsarin.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) reshen jihar Kwara, Jonathan Owoade, ya ce an kai wadanda suka jikkata da gawarwakin zuwa babban asibitin Ilorin da kuma asibitin Garin Alimi.
“Hatsarin ya shafi wata motar bas mai kujeru 18 kuma yakamata ta kasance tana dauke da fasinjoji 14 ne saboda ka’idojin hana ya duwar cutar COVID-19. Amma mutane 18 suka zauna a cikin Motar ciki har da yara. Wannan ne ya sa muka yi ta gargadi akai-akai game da daukar ka yayyakin da suka wuce gona da iri da kuma gudun wuce gona da iri,” in ji shi.
Ya godewa ma’aikatar lafiya ta jihar bisa samar da karin motocin daukar marasa lafiya yayin aikin ceto