Shugaban cocin United Church of Christ in Nigeria (HEKAN), Rabran (Dr.) Amos G. Kiri, a ranar Lahadi, a Kaduna, ya yi gargadin cewa tsawaita yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta yi, na iya haifar da karuwa aikata laifuka a kasar.
Ya bayyana haka ne a taron shekara shekara na na Cocin HEKAN karo na 56, wanda aka gudanar a Kaduna, ranar Lahadi.
Ya ce idan aka bar daliban da suka saba karatu da sauran ayyukan karatu suna yawo a gari, shaidan zai iya dawo da su, saboda rashin abunyi, shaidan zai iya amfani dasu.
Reverend Kiri ya lura cewa yawan zamansu a gida bazai harfar da da Mai Ido ba ga wasu al’ummomi.
Don haka ya yi kira ga kungiyar ASUU da gwamnatin tarayya da su gaggauta tattaunawa domin kawo karshen yajin aikin da suke yi.
Ya ce muddin dalibai za su ci gaba da zama a gida, ba tare da wani abin yi ba, za a iya fara shigar da su cikin kungiyoyin asiri da kuma muggan kwayoyi.
“Abin baƙin ciki shine, da yawa daga cikin mutane, masu kirkire-kirkire da shugabanni da na gaba an yi musu sihiri kuma sun shiga cikin ayyukan shaiɗanu da ɓarna waɗanda ke cutar da lafiyarsu da lalata rayuwarsu,” in ji shi.