Shugaban kasar Sri Lanka, Gotabaya Rajapaksa, a ranar Litinin, ya mika goron gayyasa ga daukacin jam’iyyun siyasa da su shiga cikin gwamnati domin lalubo hanyoyin warware rikicin da ke faruwa a kasar.
Gayyatar ta zo ne sa’o’i bayan da majalisar ministocin kasar suka yi murabus daga mukamansu, biyo bayan zanga-zangar da aka yi kan karancin mai.
A cikin wata sanarwa da sashen yada labarai na shugaban kasar ya fitar, ya ce rikicin da ake fama da shi a halin yanzu ya samo asali ne daga wasu dalilai na tattalin arziki da kuma wasu sauye-sauye da duniya ta tsinci Kanta a ciki.
“Ya kamata Sri Lanka ta sami mafita a cikin tsarin dimokuradiyya, la’akari da wannan wata bukata ta kasa ce, lokaci ya yi da za a yi aiki tare don kare dukkan ‘yan kasa da kuma al’ummomi masu zuwa cikin kasar.
Sanarwar ta ce “Shugaban ya gayyaci dukkan jam’iyyun siyasa da ke da wakilci a majalisar dokokin kasar da su taru domin karbar mukaman ministocin da za a yi amfani da su wajen samar da mafita ga wannan rikicin na kasa.”
Gwamnan Babban Bankin Sri Lanka, Ajith Nivard Cabraal, shi ma ya mika takardar murabus dinsa ga Shugaba Rajapaksa a ranar Litinin.
Sri Lanka ta shafe kwanaki tana fuskantar zanga-zangar jama’a , yayin da suke cigaba da kira ga matakan gaggawa da gwamnati ta dauka don magance matsalar durkushewar tattalin arziki a kasar.
An ayyana dokar ta baci a Sri Lanka a ranar Juma’a kuma dokar hana fita ta sa’o’i 36 ma tuni ta fara aiki da maraice washegari, amma, an janye shi a safiyar yau Litinin.
Comments 1