By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Osun, a ranar Lahadin da ta gabata, ta kama wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne,mai suna Malami Muhammad, yayin da wani, Babuga ya tsere da raunin harbin bindiga bayan da ya yi kokarin yin garkuwa da wani.
A cewar jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda PPRO Yemisi Opalola, an kama Muhammad ne a wani matsugunin Fulani da ke unguwar Erefe, kan titin Ondo, Ile-Ife, bayan wani artabu da bindiga.
2023: Dalilin Da Yasa ‘Yan Najeriya Ba Zasu Iya Amincewa Da ‘Yan Kabilar Igbo Ba – Apostle Suleman
Opalola, ya bayyana cewa, an ceto wanda lamarin ya shafa Muhammad Gembu ba tare da wani rauni ba, tare da taimakon wasu Fulani ’yan banga a cikin al’umma, ya bayyana cewa a lokacin da suke musayar wuta ne Babuga ya kaucewa kama shi, ya gudu daga wurin.
A cikin sanarwar ya ce, “Rundunar ‘yan sandan jihar Osun a fafutukar da ta ke na ganin jihar ba ta zama mafakar ‘yan ta’addan da za su yi barci ba, ta kama wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne mai suna Malami Muhammad ‘m’, yayin da daya kuma ya samu raunin harbin bindigu.
“A takaice dai gaskiyar lamarin ita ce, a ranar 17 ga watan Afrilu, 2022 da misalin karfe 11:30 na safe, mai shigar da karar ya kawo rahoto a ofishin ‘yan sandan ‘C’ Division, Aganhun, Ile-Ife cewa, wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka zo yankinsu a matsugunin unguwar Fulani, Erefe.dake kan titin Ondo Ile-Ife da misalin karfe 00:15 na safiyar wannan rana, kuma sun yi garkuwa da wani Muhammed Gembu.
“Nan da nan ’yan sanda suka samu rahoton, jami’an tsaro suka shiga kai farmaki, suka kama wani da ake zargi, Malami Muhammad bayan harbin bindiga, yayin da wani Babuga, wanda har yanzu ba a san sunan sa ba ya samu rauni sosai sannan ya tsere.
Haka kuma an kubutar da wanda abin ya rutsa da shi ba tare da jin ta bakinsa ba tare da taimakon Fulani ’yan banga a cikin al’umma.”
“Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Osun, wanda ya bukaci jama’a da su rika baiwa ‘yan sanda hadin kai a kodayaushe wajen bayar da bayanai masu amfani domin taimakawa wajen kamo masu aikata laifuka a jihar, ya kara da cewa wanda ake zargin za a gurfanar da shi gaban kotu bayan kammala bincike.
Comments 2