By Abbas Yakubu Yaura
An tura wani sabon Kwamandan hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) reshen jihar Kwara.
Kwamandan rundunar mai suna Fredrick Ade Ogidan wanda ya fara aiki, ya gaji Jonathan Owoade wanda ke kan hanyarsa ta zuwa Fatakwal shiyya ta 6 bayan karin girma da aka yi masa kwanan nan.
A cewar wata sanarwa da babban kwamandan kula da zirga-zirgar ababen hawa, Dapo James ya fitar ranar Laraba, ya ce har zuwa sabon nadin nasa,kwamanda Ogidan shi ne shugaban ayyuka na sashin jihar Kaduna.
Sanarwar ta kara da cewa Ogidan zai fara ziyarar jami’an sa maza da mata da masu ruwa da tsaki bayan kammala ayyukan sintiri na musamman na Sallah.
Kazalika yayi alkawarin yin aiki tare da masu ababen hawa dan rage ya waitar samun afkuwar haddura a jihar.
A cewar sa yana kira ga direbobi dasu dinga bin ka’idojin tuki ayayin Da suke gudanar da sana’ar su ta tuki.
Ogidan ya kara da cewa ba zasu lamunci halin rashin ko inkula da wasu direbobi suke Yi ba wajen duba lafiyar abin hawansu.
Comments 1