Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da kudirin 2022 na rabon kudade da ka’idoji na manyan makarantun gwamnati a fadin kasar nan.
Babban Sakatare na Asusun Tallafawa Manyan Makarantu (TETFund), Arch. Sunday Echono, ne ya bayyana hakan yayin da yake karbar bakuncin kwamitin shugabannin jami’o’in Najeriya (CVCNU) a Abuja ranar Alhamis.
An amince da kudin ne a daidai lokacin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ke ci gaba da yajin aikin.
Echono ya ce za a gudanar da taron dukkanin cibiyoyin da za su amfana nan da mako mai zuwa don yin mu’amala da su tare da yin takaitaccen bayani kan sauye-sauyen da aka amince da su don aiwatarwa.
Ya kuma tabbatar da kudirin TeFund na ci gaba da samar da sauye-sauyen da ake bukata a fannin, tare da kara ba da muhimmanci kan abubuwan da suke yi musamman a fannin bincike, ICT da kuma a fannin karfafa al’adun karatu a cikin al’ummarmu ta hanyar buga littattafai.
Tun da farko, shugaban hukumar ta CVC, Farfesa Samuel Gowon Edoumiekumo, ya ce kungiyar CVCNU na aiki kafada da kafada da hukumar TetFund domin aikewa da sabbin dabarun zamani ga manyan makarantun Najeriya.
Kungiyar ta yi kira da a sake nazarin tallafin kudade ga cibiyoyin da za su amfana don samun damar yin amfani da mujallu da wuraren ajiya na matakin bai daya don inganta iyawar bincike na ma’aikata da dalibai da kuma taimakawa wajen gina karfin ma’aikatan ilimi don samar da abun da ake fata.