By Abbas Yakubu Yaura
A daren ranar Talata ne gwamnonin jam’iyyar APC mai mulki suka yi wata ganawa domin yanke shawara kan bukatar shugaban kasa Muhammadu Buhari na ba shi damar zabar wanda zai gaje shi.
A baya dai gwamnonin sun yi taro a ranar amma sun kasa cimma matsaya kan yadda za a tunkari bukatar shugaban.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kotu Ta Daure Wani Dan Kasar China A Gidan Yari Bisa Laifin Yanyanka Takardar Naira 1000
Yayin da wasun su ke son a yi nade-nade daga tsakanin su, akwai wadanda suke ganin ya kamata a fadada har a hada da nade-nade daga waje.
Taron na daren ranar Talata yana gudana ne a gidan shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Abdullahi Adamu.
Har zuwa karfe 10:07 na dare gwamnonin na nan a wajen taron.
A dai yamma cin yau Talata ne gabanin zaben fidda gwani na jam’iyyar APC, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci gwamnonin da aka zaba a tsarin jam’iyya mai mulki da su ba shi damar zabar wanda zai gaje shi.
Shugaban ya mika wannan bukatar ne a jawabinsa yayin wata ganawa da ya yi da kungiyar gwamnonin a Abuja ranar Talata.
A cewar Buhari, an bai wa gwamnonin jihohin damar zabar wadanda zasu gaje su, inda ya nemi su ba shi damar yin hakan a matakin tarayya.
Buhari ya ce, “Bisa tsarin da aka kafa na cikin gida na Jam’iyyar da kuma tunkarar taron nan da ‘yan kwanaki, don haka ina neman goyon bayan Gwamnoni da sauran masu ruwa da tsaki wajen zabar magajina, wanda zai tashi daga mulki. Tutar jam’iyyar mu domin zaben shugaban kasar tarayyar Najeriya a 2023.
“Mun bai wa gwamnoni tikitin sake tsayawa takara ko kuma damar zabar wadanda za su gaje su; ku ba ni damar zabar magajina.”