By Abbas Yakubu Yaura
Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, reshen jihar Legas, ta gabatar da wani dan kasar Chana mai suna Li Lei Lei a gaban kutu inda ta yanke masa hukuncin daurin shekaru biyu a gidan kaso bisa laifin yan yanka ta kardar kudin Najeriya kamar nama.
Mai shari’a I. Nicholas Oweibo na babbar kotun tarayya da ke zamanta a Ikoyi, Legas ne ya yanke wa dan kasar ta China hukunci a ranar Talata.
An gurfanar da shi ne a kan tuhume-tuhume hudu da suka shafi dusashe takardar kudin Najeriya, laifin da ke da nasaba da sashe na 21 (1) na dokar babban bankin Najeriya.
Daya daga cikin tuhumar ta ce: “Wato kai, Li Lei Lei, a ranar 17 ga watan Mayu, 2022, a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke jihar Legas, da ke karkashin ikon wannan kotun mai girma, an sameka da laifin yanyanka takardar Naira Dubu Daya (N1,000).
Wacce take dauke da lamba 947882 da Babban Bankin Najeriya CBN ya fitar kuma ya aikata laifin da ya sabawa doka kuma mai hukunci a karkashin sashe na 21 (1) na Babban Bankin Najeriya na shekarar 2010.”
A wani labarin kuma
KARANTA WANNAN LABARIN: PDP Zata Baiwa Atiku Takardar Sake Tsayawa Takarar Shugabancin Kasa Karo Na Biyu Ranar Laraba
Kwamitin ayyuka na kasa na jam’iyyar PDP ya sanar da cewa zai gabatar da takardar shaidar cin zabe ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Atiku Abubakar.
Atiku ya lashe tikitin tsayawa takarar shugaban kasa na jam’iyyar ne a babban taron kasa da aka gudanar a Abuja a ranakun 28 zuwa 29 ga watan Mayun 2022 bayan ya samu kuri’u 371.
Sakataren yada labarai na jam’iyyar na kasa, Debo Ologunagba, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce ana sa ran dukkanin gwamnoni, ‘yan takarar gwamna, masu neman shugabancin kasa, mambobin kwamitin amintattu, ‘yan majalisar dokoki ta kasa, sauran ‘yan takarar jam’iyyar da kuma duk masu ruwa da tsaki za su halacci bikin na musamman.
Sanarwar ta ci gaba da cewa taron zai gudana ne a ranar Laraba 1 ga watan Yuni 2022 da tsakar rana a sakatariyar PDP ta kasa da ke Abuja.