Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta sanar da kwashe wasu muhimman kayan zabe daga babban bankin Najeriya CBN.
Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a wani taron tattaunawa da ke gudana a cibiyar Musa ‘Yar’Adua, Abuja, yau Asabar.
Yakubu ya ce CBN ba za ta ci gaba da kula da kayan zabe tun daga zaben gwamnan jihar Ekiti ba.
Misalin jihar Ekiti, an kai duk wasu kayan da ba su da hadari zuwa Ado-Ekiti kuma suna cikin dukkanin kananan hukumomin jihar.
“Amma manyan kayyakin zaben da babban bankin Najeriya ke bayarwa a madadin hukumar, (CBN) wanda aka ajiye su a gaban bankin sannan jami’an hukumar suka su fitar da su.
“Ina so in ce tun da INEC ta fara wannan hadin gwiwa da CBN, ba mu taba fuskantar ko daya daga cikin batutuwan da suka shafi safarar kayan ba.
Hukumar ta kasance abokiyar tarayya ta gari ga bankin.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC dai na fuskantar matsin lamba kan ta yanke hulda da CBN sakamakon shigar da gwamnan babban bankin kasar Godwin Emefiele ya yi takarar neman zama shugaban kasa karkashin tutar jam’iyyar APC a zabe mai zuwa.