Ƴan Sandan sun bindige Ƴan bindiga a Anambra
Jami’an tsaro a Jahar Anambra sun hallaka wani Kwamandan Ƴan bindiga dake addabar Jahar tare da kamo wasu manyan yaran su guda biyar.
Sun kuma ceto mutane huɗu da akayi garkuwa da su a garin Neni, Ƙaramar Hukumar Anaocha ta Jahar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ƴan Sanda sun hallaka riƙaƙƙun masu garkuwa da mutane 3 a Delta
Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar Ikenga Tochukwu a jiya a Awka, yace suna aiki ne da Ƴan Sa Kai a yankin, inda suka yiwa wurin ƙawanya a ranar Lahadi, tare da ceto mutane huɗu da kama wani Emeka da ake zargi.
Ikenga yace bayan an bincike shi, Emeka ya tabbatar da aikata laifin tare da Jagorantar Ƴan Sandan zuwa inda suke ɓoye a Oba, Wanda akayi musayar wuta.
Yace wani Kwamandan Ƴan bindigar Chinedu Ajogu an bindige shi, a yayinda wasu mutane biyar da suka haɗa da Boka an kama su.