Fashewar Tankar Mai ta Kashe Mutum 1, ta lalata Dukiyoyi a Jos
Mutum ɗaya ya rasa rayuwar sa, tare da lalata Dukiyoyi da suka haɗa da Ababen hawa, da Shaguna da Makarantar Koyon kiwo ta ƙone, a ranar Alhamis da safe, bayan tankar man fetur ta faɗi a Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa dake Jahar Filato.
Marigayin ya kasance matuƙin motar ne, an gano shi ne a cikin wuta, inda lamarin ya faru.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Ɗuminsa: Moghalu ya rasa Tikitin Tsayawa Takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar ADC
Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar Filato DSP Alfred Alabo ya tabbatar da faruwar lamarin, amma bai faɗi adadin mutanen da suka ji raunuka ba, yana mai cewa tuni Rundunar take bakin ƙoƙari domin gano musabbabin faruwar lamarin.
Shaidun gani da Ido sun ce tankar ta fara ne daga cin wuta, yana mai cewa tuni an tura Jami’an kashe Gobara, da Ƴan Sanda zuwa wurin.
Wakilin Majiyar mu ya tattaro cewa lamarin ya faru da misalin ƙarfe 5 na safe a ranar Alhamis, a lokacin da Tankar tayi hatsari, da shige cikin gidan wani man fetur kusa da Makarantar Koyon Kiwo.