Da Ɗuminsa: Moghalu ya rasa Tikitin Tsayawa Takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar ADC
Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya Kinglsey Moghalu ya rasa Tikitin Tsayawa Takarar Shugaban na Shekarar 2023 a Jam’iyyar ADC.
Ya faɗi, bayan mai Mallakin Gidan Talabijin na Roots Dumebi Kachikwu ya samu nasarar lashe Tikitin Tsayawa Takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar ADC a zaɓen fidda daya wakana a Abeokuta.
Ya samu nasara ne, bayan ya kada Moghalu Chukwuka Monye, da ƴan Takara guda takwas.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari Yana Jagorantar Taron Majalisar Tsaro Ta Kasa
Kachikwu wanda shine Ƙanen tsohon Ƙaramin Ministan Man Fetur Ibe Kachikwu, ya samu ƙuri’u 977.
Moghalu ya samu nasarar zama na biyu da ƙuri’u 589, a yayinda Monye ya zo na uku na ƙuri’u 339
Comments 1