Ɗa Ɗumi-Ɗuminsa: APC ta lashe Ƙaramar Hukumar Farko a Zaɓen Ekiti
Jam’iyyar Mai Mulki ta APC a Najeriya an ayyana ta a matsayin wadda ta Lashe Zaɓen Gwamnan Jahar da a halin ake gudanarwa.
Jam’iyyar ta samu nasarar lashe Karamar Hukumar Ikere ta Jahar, wadda itace ta farko da aka fara gabatarwa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wasu Ɓata gari sun ƙone Ɓarawon Waya a Jahar Bayelsa
Kamar yadda aka sanar da sakamakon a cibiyar tattara sakamakon Zaɓe ta Ƙaramar Hukumar, Abiodun Oyebanji na Jam’iyyar APC ya samu ƙuri’u dubu 12,086, a yayinda na Jam’iyyar PDP Bisi Kolawole ya samu ƙuri’u dubu 3,789.
Sai kuma Ɗan Takarar Jam’iyyar Social Democratic party (SDP) ya zo na uku da ƙuri’u dubu 1,934.
Comments 1