Gwamna Matawalle ya naɗa Mataimaka 169, da wasu
Gwamnan Jahar Zamfara Bello Matawalle ya amince da naɗa manyan Jami’an Gwamnati 169, da Mataimaka, a wani yunƙuri na inganta haɗin kai a tsakanin Jam’iyyar APC a Jahar.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata takarda mai shafuka 9, da Sakataren Gwamnatin Jahar Alhaji Kabiru Balarabe ya fitar a ranar Asabar a Gusau.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ɗa Ɗumi-Ɗuminsa: APC ta lashe Ƙaramar Hukumar Farko a Zaɓen Ekiti
Ya sanar da cewa an naɗa Alhaji Isha Umar a matsayin Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jahar Zamfara, a yayin da Alhaji Usman Magami da Alhaji Bashir Abdullahi an naɗa su a matsayin Masu Baiwa Gwamna Shawara na Musamman.
Sauran waɗanda aka naɗa mutane 103, an naɗa su a matsayin Manyan Masu Taimakawa Gwamna na Musamman, sai mutane 28 aka naɗa su a matsayin Darakta-Janar, da Masu Taimakawa Gwamna na Musamman guda 13.
Sauran sun ƙunshi Kwamishinan Din-Din-Din guda 10, da mambobin wasu Ma’aikatu, dana Sassa, ciki har da na Hukumar kula da Hajji, da Sashen Doka da sauran su.
Sakataren Gwamnatin Jahar yace naɗin su ya fara nan take.
Wannan cigaba yazo ne bayan watanni biyu da Manyan Jiga-Jigan APC ƙarƙashin Jagorancin Matawalle, da Tsohon Gwamnan Jahar Abdul’aziz Yari, da tsohon Sanata Kabiru Marafa, suka amince suyi aiki tuƙuru domin samun nasarar Jam’iyyar a Babban Zaɓen Shekarar 2023.
Biyo bayan Sasanci, Yari da Marafa, sun samu Tikitin Tsayawa Takarar Sanatoci a yankin Zamfara ta Yamma, da ta Tsakiya.
Comments 1