Wasu ‘yan bindiga sun yi awon gaba da jami’in ‘yan sanda mai kula da karamar hukumar Nasarawa Eggon a jihar Nasarawa, CSP Haruna Abdulmalik.
Jaridar DAILY POST ta ruwaito cewa an yi garkuwa da DPO din ne a ranar Alhamis yayin da yake sintiri a hanyar Nasarawa Eggon zuwa Akwanga.
Rahotanni sun bayyana cewa, masu garkuwa da mutanen sun tuntubi iyalan mamacin, inda suka bukaci a biya su Naira milliayan biyar a matsayin kudin fansa.
Sai dai duk Kokarin da majiyar jaridar Dimokuradiyya ta yi na jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa, ASP Ramhan Nansel abun ya ci tura.
Sai dai mataimakin shugaban karamar hukumar, Benjamin Kuze ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar Vanguard