Kasa da kwanaki uku a gudanar da zaben gwamna a jihar Osun, gwamnatin jihar ta ayyana ranar Juma’a 24 ga watan Yuni a matsayin ranar da babu aiki domin baiwa ma’aikatan da har yanzu basu karbi katin zabe na dindindin ba, domin su sami damar yin hakan.
A cikin wata sanarwa da gwamnatin ta fitar a ranar Alhamis, ta ce, ta yanke shwarar yin hakan ne domin baiwa dukkan ma’aikatan gwamnati da na gwamnati damar karbar katin zaben u na dindindin, wato PVC don samun damar kada kuri’ar su a zaben gwamna da za a gudanar a ranar 16 ga watan Yulin shekarar 2022.
Hakan ya fito ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar Prince Wole Oyebamiji.
Sanarwar ta kara da cewa: “Gwamnatin jihar Osun ta amince da muhimmancin ma’aikata a tsarin dimokuradiyya, kuma tana sane da cewa hanya daya tilo da ma’aikata za su iya cimma burinsu na samar da gwamnatin da ta dace da ma’aikata ita ce ta hanyar kada kuri’unsu.
Kazalika Sanarwar ta ce, “Gwamnati ba ta son kowa ya rasa damar yin amfani da ‘yancin da kundin tsarin mulkin kasar ya ba shi, musamman yadda ya shafi rayuwar su baki daya da kuma tsaron makomarsu.”