Gwamnatin Jihar Kebbi ta fara rarrarba kayayyakin aikin gona ga , manoma 7,900 ga manoma karkashin shirin nan na KB CARES, a shirin tallafin bankin duniya.
Majiyar jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa, Za a rarrarba Kayyakin aikin da kudinsu ya kai Naira biliyan 2 zuwa manoman da ke fadin jihar nan.
Kwamishinan Noma da albarkatun kasa Alhaji Maigari Abdullahi Dakingari ne ya bayyana hakan a lokacin da yake kaddamar da rarraba kayyakin ga manoma a ofishin Hukumar bunkasa Ayyukan gona ta jihar Kebbi dake Kalgo.
Bayanai sun nuna cewa tuni kashin farko suka karbi na su kason.
Kwamishinan yace an rarraba Kayyakin ne ga ƙananan manoman domin tallafa musu da ingantatun iraruwa, magungunan feshi da takin zamani, domin rage musu illar da cutar Korona ta yi a bangaren noma.
Dakingari ya kara da cewa karkashin shirin za’a gina tituna domin samun sauƙin zirga-zirga kayyakin zuwa manya manyan garuruwa daga karkara .
Ana sa bangaren Gwamnan Jihar Kebbi wanda Kwamishinan kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki Dakta Abba Sani Kalgo ya wakilta, ya bayyana cewa baya ga Naira miliyan Ashirin da Bankin Duniya ya bayar, sun kara Naira biliyan uku, domin tabbatar da shirin ya kai wurare da dama a cikin jihar nan.
A wani labarin kumanna daban.
Tsananin Yunwa, Hawan Jini Da Damuwa Sun Hallaka Yan gudun Hijira 23 A Katsina
Kimanin mutane Ashirin da uku ne suka rasa rayukan a sanadiyar yunwa, hawan jini, damuwa a sansanin ‘yan gudun dake karamar hukumar Jibiya ta jiharKatsina.
Shugaban Sansanin sa’ad Salisu ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai jiya a karamar hukumar ta Jibiya.
Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa, A wani rahoto da kungiyar cigaban karamar hukumar Jibiya ta fitar na ranar Litinin, ya nuna cewa, akalla ‘yan gudun hijira dubu ashirin da biyu, da dari uku da sittin da biyar (22,365) daga yankunan Shimfida, Garin Maiwuya, Garin Zango, Garin Kwari da kauyukan Tsambaye suna zaune ne cikin garin Jibiya.
Yan gudun hijirar na samun mafaka ne a makarantar sakandiren ‘yan mata ta gwamnati da ke Jibiya.
Kazalika Shugaban sansanin ‘yan gudun hijirar, Sa’ad Salisu, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar ci gaban matasa na garin Shimfida, ya bayyana cewa akalla mata 35 ne suka haihu a sansanin a cikin watanni hudu da suka gabata, yana mai cewa adadin zai iya zarce haka, nan gaba kadan.
A gefe guda kuma, wani lamari mai tayar da hankali kamar yadda Salisu ya bayyana, shi ne yadda akasarin yaran da ke garin da kuma na sansanin ba sa iya samun ilimi.
Ya Kuma Kara da cewa, akwai yara sama da dubu uku (3,000) a sansanin da suka bar yankunan su da suke kuma zuwa makaranta amma yanzu ba sa iya zuwa makarantar, saboda gwamnati ba ta tanadar musu da makaranta ba a sansanin da suke zaune.
Sai dai Salisu ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta gaggauta daukar matakin maido da tsaro a cikin yankunan da harin yan bjndiga ya dai-daita, domin su koam su cigaba da ayyukan noma.
A nasa jawabin shugaban karamar hukumar Jibiya, Bishir Sabi’u ya ce gwamnati ta samar da isassun kayan agaji ga ‘yan gudun hijirar.
Sai dai Kuma a cewarsa, a kullum ana dafa musu buhunan shinkafa guda goma sha biyar, domin ciyar da yan gudun hijiran da ke zaune a sansanin.
Kana ya bayyana cewa, gwamnatinsa tana baiwa ‘yan gudun hijirar dubu dari biyu N200,000 duk mako don tallafa musu wajen gudanar da ayyukansu na yau da kullun a sansanin.