By Abbas Yakubu Yaura
Ministan cikin gida, Rauf Aregbesola, ya ce karuwar fursunonin da ke jiran shari’a na yin illa ga cibiyoyin da ake tsare da su da kuma abubuwan da ake musu na hidima.
Aregbesola, wanda ya dora laifin cunkoson gidajen yari a kan yadda ake tafiyar hawainiya a shari’a, ya bayar da shawarar cewa tun daga kama wadanda ake tuhuma har zuwa kammala shari’arsu a kotu, bai kamata wa’adin ya wuce shekara guda ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/nan-da-shekaru-30-masu-zuwa-najeriya-zata-bukaci-malamai-kusan-milyan-5-okebukola/
Ya kuma bayyana kwarin gwiwar cewa hakan na iya yiwuwa, ya kara da cewa ya kwashe watanni 42 kafin ya dawo aiki a jihar Osun amma a yanzu bai wuce shekara guda ba yana kammala shari’ar kotunan zabe.
Aregbesola ya yi magana ne a rana ta biyu a taron ma’aikatan gidan gyaran hali na Najeriya da aka gudanar a Sokoto ranar Talata.
Ministan ya ce, “Bari a samar da kwakkwaran shawarwari na ganin an samar da adalci cikin gaggawa. A lokacin da na je kotu domin neman izinina da aka sace a Osun sai da aka kwashe watanni 42 ana yi. Tsawon watanni shida da cikar wa’adin ne aka dawo da wa’adina.
“Wannan gogewar ce ta tilasta wa bangaren shari’a cewa duk wata kara kan zaben gwamna ba za ta wuce shekara guda ba kuma tun daga nan suka ci gaba da yin hakan. Don rage yawan fursunonin da ke jiran shari’a dole ne mu tabbatar da cewa daga lokacin kamawa zuwa yanke hukunci kada ya wuce shekara guda.
“Idan aka yi haka, za mu rage yawan fursunonin da ke cibiyoyin gyaran hali. Haka nan za mu iya rage tsadar farashin ciyar da su da rashin wadatattun kayan aiki.
“Idan za mu iya rage adadin fursunonin da ke jiran shari’a ta hanyar yanke wa’adin gwajin zuwa watanni 12, adadin da za mu tara daga ciyar da su zai isa ya sake inganta sabis da cibiyoyinmu.”
Aregbesola ya kuma koka da abin da ya bayyana a matsayin rashin cancantar wasu wuraren gyaran hali a fadin kasar nan, inda ya bukaci jami’an da su hada kai da al’umma domin canza fuskar kayan aikin.