Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti a ranar Juma’a ya gabatar da kasafin kudin 2020 na naira biliyan 124 ga majalisar jihar domin tabbatarwa.
Rahotanni sun bayyana cewa; kasafin kudin ya debi kashi 43 wanda ya kai naira biliyan 53.53 wajen gudanar da ayyuka ci gaba. Yayin da za a yi amfani da 71.18 da ya dauki kashi 57 wajen tattalin ayyukan da ake yi yanzu.
Gwamna Fayemi ya ce kasafin kudin da ya yi zai kawo ci gaba ga jihar. Kuma zai cimma manufofin gwamnatinsa biyar wanda ya hada da kyakkyawan shugabanci da kawo wa bangaren tattalin arziki sauyi da kuma kawo ci gaba.
Kuma
ya ce kasafin kudin zai tabbatar da ya cimma nasarar manufofin kafa
gwamnatinsa.
Da yake maida bayani, Kakakin majalisar jihar, Mr Funminiyi Afuye, ya yi fatan kasafin kudin 2020
din ya bunkasa tattalin arzikin jihar tare da kawo wa jihar ci gaba mai dorewa.