A ranar Juma’a ce, ‘yan sanda suka gurfanar da wasu abokanai su biyu a gaban kotun majistare mai daraja ta 1 da ke zama a Mpape, Abuja, inda suke zargin su da satan Keke Napep wanda aka kiyasta kudinsa a kan naira 670,000, na wani da suke yi wa aiki.
‘Yan sandan sun tuhumi Emmanuel Joseph, 28, da Muritala Audu, 18, wadanda suke zaune a qauyan Ruga, Abuja, da laifin hada baki ne da kuma sata.
Dan sanda mai gabatar da kara, Mista Stanley Nwaforaku, ya shaida wa kotun cewa, waxanda ake tuhumar sun haxa baki ne suka sace Keke Napep na wani mai suna Ibrahim Saleh.
Nwaforaku ya ce, Saleh ya kai rahoton faruwar lamarin ne ga Ofishin ‘yan sanda da ke Mpape.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Salihu Ibrahim, ya bayar da belin wadanda ake tuhumar a kan tsabar kuxi naira milyan guda kowannen su, tare kuma da mai tsayawa kowannen su shi ma a kan wannan kudin.
Alkalin ya kuma yi umurni da cewa tilas ne masu tsaya masun su kasance suna zaune ne a wajen da kotun take da hurumi a cikinsa wanda kuma wani jami’in kotun zai tantance hakan. Sannan sai ya zage sauraron karar har zuwa ranar 18 ga watan Nuwamba.