Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta umurci Hukumar Kula da Shaida katin zama dan kadmsa ta Najeriya (NIMC) da ta mika takardar shedar gaskiya (CTC) na bayanan wani mutum da ake zargi an tafi da shi birtaniya da nufin cinikin sassan jikinsa, ga babban mai shari’a na tarayya domin mika shi zuwa kasar Ingila, inda Sanata Ike Ekweremadu ya ke fuskantar tuhumar satar sassan jiki.
Bayan kama sanatan da ‘yan sandan birnin Landan suka yi, Adegboyega Awomolo, SAN, a ranar 27 ga watan Yuli, ya bukaci mai shari’a Inyang Ekwo da ya ba da umarnin a saki wasu takardu na Ukpo da ke zaune a NIMC, a hukumar Nigerian Immigration Service da Bankin Stanbic-IBTC domin yin aiki yadda ya kamata wajen kare Ekweremadu a kasar Birtaniya.
Mai shari’a Inyang Ekwo ne ya yi wannan roko.
A zaman na yau, lauyan NIMC, Muazu Mohammed, ya shaida wa kotun cewa dokokin hukumar ba su ba ta damar mika bayanan wani mutum, ga wani dan kasa mai zaman kansa.
Ya kara da cewa bisa ga dokar NIMC, ya kamata a fara mika irin wadannan bayanai ga AGF.
Awomolo dai bai yi adawa da maganar da Mohammed ya yi ba, inda ya kara da cewa AGF na da hanyar sadarwa ta diflomasiyya da hukumomin Burtaniya.
Daga nan ne mai shari’a Ekwo ya umarci NIMC da ta kai bayanai na wanda abin ya shafa da ke hannun Hukumar, ga AGF domin mika shi ga kotunan da abin ya shafa a kasar Ingila.