Daga: Abbas Yakubu Yaura
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce ci gaba da rijistar masu kada kuri’a (CVR) wa’adinta zai kare a ranar 31 ga watan Yuli, 2022.
Hukumar ta yanke wannan shawarar ne a wani zama na musamman da aka yi a ranar Juma’a.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/osun-2022-sojoji-sun-kame-shugaban-kungiyar-nurtw-na-jihar/
Alkalin zaben ya ce an kuma tsawaita atisayen zuwa sa’o’i takwas a kullum daga karfe 9 na safe zuwa 5 na yamma maimakon awa shida a kullum.
Festus Okoye, kwamishinan INEC na kasa, ya ce ci gaba da aikin zai kuma hada harda kwanakin karshen mako sabanin kwanaki biyar daga Litinin zuwa Juma’a.
Tun da farko INEC ta tsayar da ranar 30 ga watan Yuni a matsayin karshen wa’adin gudanar da rijistar masu zabe ta CVR a zaben 2023, amma daga baya hukumar ta tsawaita aikin da makonni biyu.
Hukumar ta bukaci ‘yan Najeriya da su yi amfani da sabon karin wa’adin makonni biyu don yin rijistar katin zabe na dindindin (PVCs).
“Muna rokon hakuri da fahimtar dukkan ‘yan Najeriya yayin da muke kammala atisayen da za a koma bayan babban zaben 2023,” in ji INEC.
“Mun lura cewa bayan ci gaba da aikin tun daga ranar 30 ga watan Yuni 2022, yawancin cibiyoyin rajistar sun sami karancin fitowar masu rajista.
“Da wannan tsawaitawar makwanni biyu, muna kira ga ‘yan kasa da su jira har sai ‘yan kwanaki kafin su sake mamaye cibiyoyin don yin rajista.”