Daga: Ibrahim Hassan Hausawa
Akalla mutane biyu da ake kyautata zaton masu satar babura ne suka kone kurmus a Ibadan babban birnin jihar Oyo.
Jaridar DAILY POST ta tattaro cewa wadanda ake zargin sun kone bayan sun kwace babur daga hannun mai shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/abba-kyari-yadda-na-%c9%93oye-daga-%c6%b4an-taaddan-da-suka-kai-hari-gidan-yarin-kuje/
Tunda farko Wadanda ake zargin, wanda yayi sanadiyyar fusata mazauna garin suka kama su, wanda kuma daga baya suka kona su.
Jaridar Dimokuradiyya ta tattaro cewa an kama barayin babur din ne a lokacin da suke kokarin tserewa.
Lamarin ya faru ne a General Gas da ke karkashin gada a Ibadan da yammacin yau Laraba.
An tattaro cewa an kama wadanda ake zargin ne bayan da suka yi yunkurin guduwa tare da harbin masu bin su.
Wakilinmu ya tattaro cewa wasu daga cikin mazauna garin sun ja kunnen ‘yan sanda kan lamarin.
Amma, fusatattun mazauna garin sun riga sun banka wa wadanda ake zargin wuta kafin isowar jami’an ‘yan sandan.
Sai dai duk kokarin da Jaridar Daily POST ta yi don jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Adewale Osifeso ya ci tura.
Kiraye-kirayen da aka yi masa ta wayarsa bai yi nasara ba yayin da aka aika masa da sakon kar takwana bai amsa ba har zuwa lokacin gabatar da rahoton, a yammacin Laraba.