Wata mota kirar Toyota Corolla ta murkushe wasu ’yan kasuwa uku da aka fi sani da okada, har lahira a tashar Arepo da ke kan titin Legas zuwa Ibadan a jihar Ogun.
Wakilin majiyar jardiar Dimokuradiyya ya samu labarin cewa direban motar da ke gudun wuce kima ya kutsa cikin masu baburan da ke tashar motar, suna jiran daukar fasinjoji.
An ruwaito cewa Corolla mai lamba FKJ 848 FH, babur Bajaj mai lamba WDE 184 UP, wasu babura biyu masu lamba SGM 404 VL da DED 802 VC da kuma wani babur da ba a yi rijista ba ne suka lamarin ya shafa.
Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) reshen jihar Ogun, Ahmed Umar ya tabbatarwa manema labarai faruwar lamarin a Abeokuta.
Umar ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da karfe 12:30 na daren ranar Alhamis.
Ya bayyana cewa mutane takwas ne – maza bakwai da mace daya – suka yi hatsarin, inda ya ce mutane hudu sun samu raunuka yayin da mutum daya ya samu rauni.
KARANTA WANNAN LAABRIN: Sojoji Sun Tabbatarwa Buhari Sabuwar Dabarar Magance ‘Yan Bindiga Da ‘Yan ta’adda – NSA
Ya ce wasu mutane uku masu tuka babur ne suka mutu a hadarin.
Umar ya ce an kai wadanda suka jikkata zuwa Asibitin Beachland da kuma asibitin ROA da ke Arepo, yayin da biyu daga cikin wadanda suka mutun kuma al’ummar Hausawa suka dauke su a Arepo domin yi musu jana’iza.
Ya kara da cewa sauran wadanda suka mutu an kai su dakin ajiye gawa na Asibitin Divine Touch da ke Arepo.
Umar ya shawarci masu ababen hawa da su bi ka’idojin zirga-zirga.
A wani labarin kuma na daban.
Surukina Tinubu Shekarun Shi 86, Bai Cancanci Zama Shugaban Kasa Ba – Tee Mac
Shahararren mai kada sarewa, Tee Mac Omatshola Iseli ya bayyana dalilan da ya sa dan takarar shugaban kasa karkashin jnuwar jam’iyar APC, Bola Tinubu, bai kamata ya zama shugaban Najeriya ba.
Tee Mac yayi ikirarin cewa Tinubu yana da shekaru 86 don haka kuma bai cancanci zama shugaban Najeriya ba.
Tsohon shugaban kungiyar mawaka ta Najeriya, PMAN, ya ce shi da matar Tinubu, Remi ’yan uwa ne amma ya daina goyon bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a 2015 saboda ya nemi ‘yan Najeriya su zabi shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Da yake mayar da martani ga wani ma’abocin Facebook, Yemi Olakitan, wanda ya bayyana goyon bayansa ga Tinubu, Tee Mac ya ce ya daina ziyartar gidan Tinubu da goyon bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC duk da kasancewarsa suruki.
Ya wallafa cewa: “Ya kai Yemi, kowa zai iya zaɓar kowane ɗan takara amma mai hankali zai yi wa kansa tambayar: shin na zaɓa wanda ya dace! Shin mutumin ya cancanta? Shin mai gaskiya ne? Shin yana gaya mana gaskiya game da shekarunsa, tarihinsa, da kuma yadda ya sami kuɗinsa? Shin mutumin yana da koshin lafiya yana da shekaru 86, zaj iya ɗaukar aikin ƙasar da ta lalace gaba ɗaya?
“Ka ga, Tinubu surikina ne. Matarsa Remi ƙanwata ce, mahaifiyarta Itsekiri da mahaifiyata Itsekiri yan uwan juna ne. Na san Tinubu tun tsakiyar shekarun 80s da kaina har ma na shirya shi ya zauna a gidan ubana (SIR MOBOLAJI BANK-ANTHONY) a Landan lokacin da ya tafi gudun hijira.
“Na daina ba shi goyon baya, na daina ziyartar dangisa da sauransu lokacin da ya tallata wa al’umma shugaba Buhari a shekarar 2015.
“Don haka Ina shawartar al’umma cewa wannan mutumi bai cancanci zama shugaban mu ba” inji shi