Daga: Abbas Yakubu Yaura
Shugabar mata ta jam’iyyar APC ta kasa, Dr. Betta Edu ta yi ikirarin cewa matasa musamman mata ne za su tantance wanda zai lashe zaben shugaban kasa a 2023.
Ta bayyana hakan ne a wajen wani taro da kungiyar APC Young Progressive Women Forum ta shirya a Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rikicin PDP: Okowa, Ortom Sun Roki Wike Kan Bukatar Ayi Sulhu Kafin Babban Zaben 2023
“Zaben da ke tafe dai matasa ne musamman mata. Dole ne dukkan mu a shirye muke mu tara kuri’u sama da miliyan 20 domin neman dan takararmu, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu domin ya lashe zaben shugaban kasa.
“Mun fara aikin ‘yan mata 1000 a kowace unguwa.
“Waɗannan matan za su ɗora wa ƴan mata a wata unguwa da aka ba su. Dole ne mu sanya lamarin ya faru a sassanmu daban-daban a duk jihohin kasar nan,” in ji ta.
A Wani Labarin Kuma Mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Gwamna Ifeanyi Okowa ya yi kira ga takwaransa na jihar Ribas, Gwamna Nyesom Wike kan bukatar a yi sulhu na gaskiya a kan batutuwa masu da ke dagula jam’iyyar.
Mista Okowa ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan ganawar sirri da Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue a masaukin gwamnatin jihar Benue da ke Asokoro, a Abuja.
Ya kara da cewa, jinkirin da aka samu na ganawa da Gwamna Wike, ya biyo bayan tafiyar sa ne zuwa kasar waje, kuma a yanzu da ya dawo jam’iyyar da dan takararta na shugaban kasa za su yi duk mai yiwuwa don ganin sun sasanta da shi.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, A nasa bangaren, Ortom ya ce shawarar da ya bayar kan bukatar gamsar da Gwamnan Jihar Ribas ita ce hanya mafi dacewa da a bi.
Ya ce ya na bayan yunkurin sasantawa da Wike domin maslahar jam’iyyar baki daya domin dole ne dukkan hannaye su kasance a dun kule kafin zaben 2023 mai zuwa.