Kwanaki biyu bayan da gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya bayar da umarnin rufe makarantu sakamakon rashin tsaro, ya sake magantuwa dangane da yadda ‘yan ta’addan da suka mamaye jihohin Kaduna Zamfara, Neja Kebbi da sauran jihohin jihar suka yi kaura zuwa cikin jihar Nasarawa.
A jiya ne Gwamna Sule ya kira taron gaggawa na majalisar tsaro, da nufin duba yanayin tsaro a jihar biyo bayan rahotannin da ke cewa ‘yan ta’adda sun shiga cikin jihar, bayan sunyi kaura wasu daga cikinsu daga wasu sassan kasar nan.
Babban taron tsaro na gaggawa da aka gudanar a gidan gwamnati a cewar gwamnan shi ne daukar matakan da suka dace duba da yanayin tsaro a kasar nan musamman a babban birnin tarayya Abuja.
DUBA WANNAN LABARIN: Sanata Sankara Ya Nesanta Kansa Daga yunkurin masu tsige Buhari
Ya kara da cewa a kwanan nan sama da fursunoni 800 suka tsere daga gidan yarin Kuje, don haka akwai bukatar kara Zage Damtsen.
Gwamnan ya bayar da sanarwar ne a wajen fadada taron tsaro na cewa an gano wasu gungun ’yan ta’adda da ake zargin sun tsere daga jihohin Neja, Zamfara, Kebbi da Kaduna, a Rugan Juli da Rugan Madaki a karamar hukumar Karu, da ke wajen babban birnin tarayya.
Gwamnan wanda ya tabbatar da cewa rahotannin tsaro da aka samu sun nuna cewa kwararowar ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan fashi ne ba wai kawai ya kara yawaitar sace-sacen mutane a cikin watanni biyu da suka gabata ba.
Gwamnan ya ce bisa wannan ci gaba, tare da kokarin gwamnatinsa, ya zama wajibi a kira taron, da nufin sabunta dabarun tunkarar kalubalen.
Yayin da yake karin haske kan dalilin da ya sa gwamnatin jihar ta yanke shawarar rufe makarantu, Sule ya jaddada cewa matakin ya biyo bayan wata ganawa da wasu shugabannin tsaro da suka yi tun farko kan yadda ‘yan ta’adda ke tururuwa zuwa jihar.
Gwamnan ya yabawa jami’an tsaro da ke aiki a jihar, da kuma sarakunan gargajiya bisa irin rawar da suke takawa wajen magance matsalolin tsaro.
Jim kadan bayan kammala taron, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Adesina Soyemi, shugaban karamar hukumar Lafia, Hon Aminu Muazu Maifata, Etsu Karu, HRH Pharmacist, Luka Panya Baba da Chun Mada, HRH Samson Gamu Yare, sun yi wa manema labarai karin haske game da sakamakon zaben taron tsaro na gaggawa.