Shugaban Kwamitin Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a na Majalisar Dattawa, Danladi Sankara, ya nesanta kansa da shirin tsige Shugaba Muhammadu Buhari.
Sanata Sankara wanda guda ne cikin sanatocin jihar Jigawa a majalisar dattawa, ya yi watsi da rahoton da ke alakanta shi da wani shiri da wasu Sanatoci ke yi na tsige Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan.
A ranar Larabar da ta gabata ne Sanatocin ‘yan adawar suka bai wa Buhari wa’adin makonni shida kan ya magance matsalar rashin tsaro ko kuma a tsige shi.
Daga bisani Sanatocin sun fice daga zauren majalisar suna rera taken “Dole ne Buhari ya tafi” lokacin da shugaban majalisar ya hana yunkurin yin muhawara kan batun.
KARANTA KARIN WANNAN LABARIN: Likitocin jihar Osun sun tsunduma yakin aiki
Batun tsige shi ya zafafa ne a ranar Alhamis lokacin da ‘yan jam’iyyar PDP a majalisar wakilai, suka hada kai da takwarorinsu a majalisar dattawa.
Matakin da ‘yan majalisar suka dauka na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun tashe-tashen hankula a babban birnin tarayya Abuja dangane da hare-haren ta’addanci.
Sanata Sankara, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, ya ce babu wani lokaci da aka tuntube shi ko kuma a yi masa katsalandan a cikin shirin.
A cewarsa, abin da ya fi daukar hankali a wannan lokaci mai cike da kalubale shi ne balaga da fahimtar shugabanni da jama’a don ganin Najeriya ta shawo kan matsalar tsaro da tabarbarewar tattalin arziki. Ya ce: “Yana da matukar muhimmanci ga shugabanni su binciko hanyoyin da za a iya magance matsalar rashin tsaro.
“Bai dace mu kara zafafa harkokin siyasa ba a lokacin da ya kamata mu hada kai don gano hanyoyin magance matsalolin tattalin arziki da rashin tsaro, Hakki ne na hadin gwiwa a kan shugabanni da jama’a.