Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba a ranar Asabar din nan da yamma sun yi wa jami’an tsaro kwanton bauna a unguwar Jidda-Bassa da ke karamar hukumar Ajaokuta a jihar Kogi, inda suka kashe ‘yan sanda uku da ‘yan banga biya wato yan bijilanti.
An tattaro daga wata majiya mai tushe da ta nemi a sakaya sunanta cewa wasu mutane da ke zaune a unguwar Jidda-Bassa sun kai rahoto ga jami’in ‘yan sanda na shiyya cewa wasu mutanen da ba a san ko su waye ba sun kai hari gonakinsu, suna kwashe kayan amfanin gona.
Majiyar ta ci gaba da cewa baturan yan sanda yankin DPO ya tattaro wasu daga cikin mutanensa da ’yan banga zuwa wurin, amma kafin su isa gonar, wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka yi musu kwanton bauna.
Majiyar ta ce yayin harin an kashe ‘yan sanda uku da ‘yan banga biyar wato yan bijilanti.
KARANTA WANNAN: https://dimokuradiyya.com.ng/gwamnatin-nasarawa-ta-tabbatar-da-kwararar-%c6%b4an-bindiga-a-jihar/
Majiyar ta kara da cewa an ajiye gawarwakin wadanda aka kashe a dakin ajiye gawa na Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya.
A halin da ake ciki, gwamnatin jihar Kogi ta sha alwashin kamo wadanda ke da hannu a kisan.
Mai baiwa gwamnan jihar Kogi shawara kan harkokin tsaro Jerry Omodara ne ya bayyana haka yayin da yake tabbatar da faruwar harin a wata zantawa da ya yi da wakilin gidan talabijin na Channels ta wayar tarho a Lokoja.
Ya ce gwamnatin jihar za ta dauki matakan da suka dace domin kamo alhakin lamarin tare da nuna cewa duk wadanda ke da hannu a kashe-kashen ba shakka za a kama su.
Omodara ya kara da cewa gwamnatin jihar na yin iya bakin kokarinta wajen ganin an dakile masu aikata laifuka a jihar.