Daga: Abbas Yakubu Yaura
A wani bangare na kokarin dakile annobar COVID-19 a jihar Gombe, Gwamna Inuwa Yahaya ya ware Naira biliyan 8.5 don tallafawa manoma 288, 700 da ‘yan kasuwa da kuma gidaje da annobar ta shafa.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin kaddamar da shirin farfado da tattalin arzikin jihar Gombe na COVID-19 (GO-CARES) a karamar hukumar Yamaltu/Deba da ke jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ziyarar Da Muka Kaiwa Wike Bata Siyasa Ba Ce – Babachir, Dogara
Ya ce shirin ya yi dai-dai da shirin gwamnatin sa na bunkasa jarin bil Adama.
“Inda ya kara da cewa an tsara shi ne musamman domin fadada hanyoyin samar da tallafin rayuwa, samar da abinci da kuma samar da tallafi ga matalauta da marasa galihu a cikin al’ummomin da annobar ta lalata hanyoyin rayuwarsu.
Ya ce tasirin COVID-19 ga tattalin arziki da rayuwar jama’a yana da yawa don haka akwai bukatar gwamnati ta kawo agaji ga wadanda abin ya shafa.
A cewarsa, za a bayar da Naira biliyan 3.4 daga cikin kasafin kudin domin tallafa wa talakawa da marasa galihu da tallafi da ayyukan yau da kullum.
Sannan yace za a yi amfani da Naira biliyan 3.4 wajen tallafa wa manoma da kayan amfanin gona domin kara samar da abinci da inganta ayyukan yi na sarkar darajar wadatar abinci.
“Za a raba Naira biliyan 1.7 ne a matsayin tallafi ga ma’aikatan jinya don tallafawa ayyukansu da kuma taimaka musu wajen murmurewa daga dimbin asarar da aka yi a lokacin annobar,” inji shi.