Kwallon da Jordan Ayew ya ci ce ta haramta wa Arsenal maki uku a wasan mako na 22 tsakaninta Crystal Palace.
Kyaftin Pierre-Emerick Aubameyang ne ya fara ci wa Arsenal kwallo kuma a minti na 67 aka kore shi daga wasan bayan ketar da ya yi wa Meyer a gefen hagu.
Katin gargadi aka fara ba shi kafin daga baya na’urar VAR ta sauya hukuncin zuwa na kora, abin da ya sa Aubameyang ya zama dan wasan Arsenal na uku da ya ci kwallo kuma aka kore shi daga wasan a tarihi.
Ayew ya farke kwallon ne bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, inda kwallo ta daki jikin Luiz kuma ta canza wa mai tsaron raga Leno tunani.
An ci kwallo 28 a karawa tsakanin kungioyin biyu a wasa bakwai na baya-bayan nan amma wannan karon kwallo biyu kacal aka ci, duk da cewa Tomkins da Nicolas Pepe sun kokarta wa kungiyoyin.
Wanann ne wasan Premier na hudu a jere da Palace ta buga da Arsenal ba tare da rashin nasara ba – karon farko kenan (canjaras 1, nasara 3).
Ita kuwa Arsenal ba ta ci wasa ko daya ba cikin 15 na waje da ta buga tsakaninta da kungiyoyin da suke samanta a teburi (canjaras 4, rashin nasara 11), tun Satumban 2015.
Palace tana matsayi na tara da maki 29, Arsenal na biye mata a mataki na 10 da tazarar maki daya tsakaninsu.