An yi zargin an kashe makiyaya shida tare da Ɓacewar wasu bakwai a ƙauyukan Mongi da Langai da ke Ƙaramar Hukumar Mangu ta jihar Filato bayan wani hari da wata kungiya mai suna Ƴan Babeli da ke Bauchi ta kai.
Shugaban Ƙungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah ta Najeriya (MACBAN) na jiha, Malam Nura Abdullahi, ya tabbatar wa Daily Trust faruwar lamarin a jiya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dalilin da yasa Kwankwaso ke goyon bayan Tinubu ya zaman Shugaban Ƙasa – Deji Adeyanju
Ya ce kungiyar ta mamaye al’ummomin ne a ranar 22 ga watan Yuli, inda suke farautar mutane da sunan ta’addanci, inda ya bayyana cewa ƴan kungiyar sun kama wasu Fulani ne suka kai su wani daji inda suka kashe su.
Shugaban na MACBAN ya ce an kama mambobinsu 13 sannan an gano gawarwakinsu shida a cikin daji yayin da sauran ba a gansu ba.
Ya ce, “Daga ranar 23 ga watan Yuli zuwa 31 ga watan Yuli, mun binne mutane shida. Waɗanda aka kashe ba su da laifi kuma bakwai ba a gansu ba. Biyu daga cikin waɗanda aka kashe sun fito ne daga Mongi kuma hudu daga cikin Al’ummar Langai ne. Ɗaya daga cikin waɗanda aka kashe akwai wani Ɗalibi. Akwai kuma wani mutum mai Shekaru 65 da aka kashe shi ma.
“Wannan ba abin yarda ba ne. Yana da mummunan aiki na tsari mafi girma. Adalci ne na Daji kuma ba za mu lamunta da shi ba. Idan sun zarge su da yin garkuwa da su, da a kai su Kotu bayan an kama su. Idan aka same su da laifin, a yanke musu hukunci.
“Bayan sun kashe su, sun sace dukiyoyinsu da kudadensu. Suka dauki Babura. Muna kira ga hukumomin tsaro da su dauki mataki. Na sanar da Barikin GOC 3 akan lamarin,” inji Abdullahi
Da aka tuntubi kakakin Ƴan sanda na Bauchi, Ahmed Wakili, ya ce “Rundunar Jihar Filato ce ke da hurumin magana a kai.”
Da aka shaida wa kungiyar Ƴan Babeli daga Bauchi, ya amsa da cewa, “Ba mu san kungiyar da suke zargin ba. Idan sun san mutanen da suka kashe membobinsu, to su bayyana mana su. Domin an ajiye gawarwakin a Bauchi, hakan ba yana nufin an kashe su ne a Bauchi ba.”
Amma da aka tuntubi Kakakin Rundunar ƴan sandan Jihar Filato, DSP Alabo Alfred, ya ce, “Ban samu labari kan lamarin. Idan na samu, za ku ji.”