’Yan ta’addan sun sako mutum shida ’yan gida daya daga cikin fasinojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna da ke hannunsu.
Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta gano cewa an sako iyalan ne bayan fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya shiga tsakani.
Mawallafin Jaridar Desert Herald da ke Kaduna, Tukur Mamu, ya ce Gumi ne ya shiga tsakani bayan ya tattauna da ’yan ta’addan a karon farko tun bayan faruwar lamarin a ranar 28 ga watan Maris, 2022.
“Ya roke su da su sako kananan yaran da iyayensu da ba su ji ba, ba su gani ba; An gano cewa yanayin lafiyar biyu daga yaran ya tabarbare tun bayan bulalar da ’yan ta’addar ya wa shafi mahaifinsu,” inji shi.
CG Ya Shawarci ‘Yan Kasuwar Katako Da Su Samar Da Wuraren Kashe Gobara
Mahaifin yaran hudu ma’aikaci ne na Hukumar Majalisar Dokoki ta Kasa, amma dai babu wani shiga tsakani da Hukumar ko Majalisar ta yi tun lokacin da abin ya faru.
Sunayen ‘yan uwa 6 da aka saki sune Abubakar Idris Garba, wanda shine mahaifin ‘ya’yan hudu, matarsa Maryama Abubakar Bobbo da babban dansu, Ibrahim Abubakar Garba mai shekaru 10.
Sauran sun hada da Fatima Abubakar Garba ’yar shekara 7, Imran Abubakar Garba mai shekara 5 sai kuma Zainab Abubakar Garba mai shekara daya da rabi kacal.
Mijin, Abubakar dan Manjo Janar Idris Garba ne mai ritaya Janar Garba wanda dan asalin jihar Neja ne kuma tsohon shugaban mulkin soja na jihohin Kano da Benue a zamanin gwamnatin tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Babangida.
Garba ya roki gwamnati da ta tabbatar da sakin yaronsa, surukarsa da jikokinsa.