Da dumi-dumi: Tsohon Shugaban Shirin Sulhu na Neja Delta, Dokubo ya rasu
Farfesa Charles Dokubo, tsohon shugaban shirin afuwa na Ƙasa, PAP, ya rasu.
DAILY POST ta samu cewa Dokubo ya rasu ne bayan gajeriyar jinya da ya yi a yammacin ranar Laraba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dole ku Binne gawa a cikin Kwanaki 3, IPOB ga Ƴan Kudu
An haifi tsohon shugaban Hukumar afuwa a garin Abonnema, karamar hukumar Akuku Toru ta jihar Ribas a ranar 23 ga Maris 1952.
Dokubo ya yi karatun firamare da sakandare a garin Abonnema.
Ya yi matakinsa na karantun Kwalejin Fasaha ta Huddersfield da ke Yammacin Yorkshire. Daga 1978-1980, Dokubo ya samu gurbin shiga Jami’ar Teesside da ke Middlesbrough, inda ya yi kwas a fannin Tarihi da Siyasa na Zamani, sannan aka ba shi BA [Hons] a Jami’ar Bradford.
Ya kammala digirinsa na biyu a fannin nazarin zaman lafiya, kafin ya ci gaba da digirinsa na uku a fannin makamin nukiliya.