2023: Ni ba mai Biyayya bace ga Peter Obi, Amma zanyi mashi aiki yaci Zaɓe- Aisha Yesufu
Wata mai fafutukar jin dadin jama’a, Aisha Yesufu, ta dage cewa ba ta biyayya ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Mista Peter Obi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kwankwaso Ya Ci Amanata– Inji Shekarau
Yesufu a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter a daren ranar Alhamis, ta ce amincinta ga Najeriya ne kuma a shirye take ta soki Obi.
Sai dai kuma ta bayyana cewa za ta yi wa tsohon gwamnan jihar Anambra aiki domin ya lashe zaben shugaban kasa a 2023.
“Don haka mun fito fili, aikina na daya shine na soki Peter Obi @PeterObi duk wani yunkuri da ya kamata a soke shi.
“Na biyu shi ne a ba shi goyon baya don ya ci zabe, lura da cewa ta na bukatar wanda zai sa Najeriya ta yi aiki.
“Amincewata ga Najeriya ce, ba Peter Obi ba. Ina bukatan wanda zai iya yiwa Najeriya aiki.!” Yesufu ta rubuta.
A wani labarin kuma:Mutane Bakwai Sun Mutu A Wani Hatsarin Mota A Ekiti
Kwamandan hukumar kiyaye afkuwar hadura ta kasa FRSC reshen jihar Ekiti, Mista Olusola Joseph, ya bayyana a ranar Alhamis din nan cewa, mutuwarsu ta biyo bayan wani karo da wata motar bas mai dauke da mutane 18 da wata mota kirar Toyota.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Ya bayyana cewa hatsarin ya afku ne a daidai lokacin da direban daya daga cikin motocin ke kokarin kaucewa wani rami a kan hanyar.