Gwamnatin tarayya ta bayyana rashin jin dadinta game da cin zarafi da kyama da ‘yan kasarta da wasu bakaken fata ‘yan Afirka ke fuskannta a kasar Chana.
Ministan harkokin wajen Nijeriya, Geofrey Onyeama, ya ce kasar ba ta ji dadin labarin da ta samu ba kan wariyar da ake nuna ma bakaken fata dangane da cutar korona.
A tattaunawarsa da takwaransa na Chana Zhou Pingjian, ministan ya ce abubuwan da ke faruwa kan bakaken fata a Chana ba abin yarda bane, kuma abin a yi Allah-wadai ne.
Sai dai wannan na zuwa ne jim kadan bayan da wasu rahotanni daga Chana suka nuna cewa daruruwan ‘yan Nijeriya aka tilastawa barin gidajensu da Otel-Otel din da suke zaune. Kuma hakan ya biyo bayan jita-jitar da ake yadawa cewa ‘yan Afrika na dauke da cutar korona.
Hotunan bidiyo masu sosa zuciya sun yadu a kafafen sada zumunta sun nuna yadda jami’an tsaron Chana suka rika cin zarafin bakaken fata.