Sakamakon rashin kawo karshen cutar Korona a Nijeriya duk da garkame tasoshin jirgin sama na kasar, hakan ya sanya gwamnatin tarayya ta sake kara wa’adin mako biyu inda tasoshin jirgin saman za su ci gaba da kasancewa a garkame domin ganin an dakile yaduwar cutar.
Ministan jiragen sama, Hadi Sirika shi ne ya bayyana hakan a Abuja a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na Hukumar, James Odaudu ya sanyawa hannu. Inda ya tabbatar da cewa sun yi hakan bisa yadda shugaban kasa Buhari ya bada umurnin kara wa’adin garkamewar wanda da da farko ake sa ran a bude a ranar 23 ga watan Afrilun 2020.
Idan zaku iya tunawa gwamnatin tarayya ta rufe tasoshin jiragen saman Murtala Muhammed International Airport, dake Legas da Nnamdi Azikiwe International Airport dake Abuja a ranar 23 ga watan Maris din 2020 har na tsawon wata daya. Inda a yanzu kuma aka kara wa’adin mako biyu.