Rundunar sojin saman Najeriya da ke aiki a jihar Zamfara ta kashe wani shugaban ‘yan bindiga, wanda aka fi sani da Dogo Rabe da wasu ‘yan kungiyarsa sama da 45 a dazuzzukan Zamfara.
Daily Post ta ruwaito cewa, Jami’an rundunar sojin saman Najeriya sun yi ruwan bama-bamai a sansanonin ‘yan bindigar da ke tsakanin al’umomin Zurmi da Birnin Magaji a jihar Zamfara da Jibia a jihar Katsina, kamar yadda wata majiyar tsaro ta bayyana.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamna Wike ya sake tafiya Europe, bayan hira da Kafofin watsa labarai
DAILY POST ta ruwaito cewa, kwanaki kadan kafin kai harin bama-baman, an kai wani hari makamancin wannan a sansanin na wani jagoran ‘yan bindiga, Bello Turji da ke unguwar Fakai a jihar, inda aka kashe ‘yan bindiga a kalla 22, yayin da Turji ya tsere da rayuwarsa.
A cewar wata majiya daga yankin, Abdulbaqi Aliyu, harin na baya-bayan nan ya yi sanadin mutuwar ‘yan bindiga a kalla 40 a yankin Birnin Magaji na jihar.
“Rundunar sojin saman Najeriya ta kai farmaki a dajin Sabon Birini Dan Ali, a karamar hukumar Birini Magaji, wanda ya yi sanadin kashe ‘yan fashin sama da 40,” inji shi.
An kai harin ne a lokacin da aka ce gungun na lodin shanun da suka sata.
“Ba a bayyana adadin mutanen da aka kashe a wannan farmakin ba saboda ‘yan bindigar sun taru a gidan wani jagoransu mai suna Dan Karami domin yin taro. Babu tabbas ko yana cikin wadanda aka kashe,” inji majiyar.
Kawo yanzu dai babu wata sanarwa a hukumance daga bakin Abdul Olaitan, kakakin rundunar sojin sama a jihar Katsina saboda bai amsa kiran wayan manema labarai ba.
A WANI LABARIN KUMA: Wani Jigo A Jam’iyyar PDP ya bayyana hanyoyi uku da za a iya tsige Ayu
Umar Sani, tsohon babban mai ba mataimakin shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a Namadi Sambo, ya bayyana hanyoyi uku kacal da za a iya tsige shugaban jam’iyyar PDP na kasa Iyorchia Ayu.
PDP dai ta sha fama da rikici tun bayan fitowar Alhaji Atiku Abubakar a matsayin dan takararta na shugaban kasa a 2023.